IQNA

23:53 - April 25, 2020
Lambar Labari: 3484744
Tehran(IQNA) wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun tona masallaci a garin Al’ara’ish na Morocco da sunan neman taska.

Shafin yada labarai na Alsabah ya bayar da rahoton cewa, a jiya wasu mutane da ba a sansu ba sun tona masallaci a garin Al’ara’ish na Morocco da sunan neman taska inda suka balle munbarin masallacin, da hakan ya kai keta alfarmar kur’ani da ke wurin.

Wannan masallacin dai yana daga cikin masallatai na tarihi a kasar Morocco, wanda aka gina shi tsawon daruruwan shekaru da suka gabata, wanda hakan ne yasa wasu ke zaton samun tsoffin abubuwa masu kima a cikinsa.

Jami’an tsro dai sun shiga gudanar da bincike kan lamarin domin gano wadanda suke da hannu wajen aikata wannan ta’asa domin gurfanar da su.

 

 

3894048

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gabata ، Morocco ، tona ، masallaci ، taska ، aka gina ، tsawon daruruwan shekaru
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: