IQNA

Dan Wasan Aston Villa Ya Ce Yana Sauke Kur’ani A cikin Watanni Biyu

14:27 - May 03, 2020
Lambar Labari: 3484759
Tehran (IQNA) Muhamd Hassa Trezeguet dan wasan kwallon kafa a Aston Villa ya ce a cikin watanni biyu yana sauke kur’ani mai tsarki.

Shafin yada labarai na yau Sabi ya bayar da rahoton cewa, a zantawarsa da tashar DMS fitaccen dan wasan kwallon kafa dan asalin kasar Masar ya ce a cikin watanni biyu yana sauke kur’ani mai girma.

Ya ce a lokacin watan Ramadan lamarin yana banbanci, inda yak an sauke kur’ani ko sau biyua  cikin wannan wata, domin ladarsa tafi yawa a wannan lokaci.

Ya kara da cewa tun yana karami yana da sha’awar wasan kwallon kafa, kuma mahaifansa ba su hana shi yin wasan ba, kuma daga karshe har ya zama daya daga cikin ‘yan wasansa kungiyar kwallon kafa na kasarsa.

Haka nan kuma ya yi ishara da muhimman aikata kyawawan ayyukan a cikin watan Ramadan, domin kuwa lokaci ne wanda ake ninninka lada ga duk wani aiki na alhairi a cikinsa.

 

3895910

 

captcha