Bisa ga al’ada mutanen kasar Masar tun daga ranar da aka ga watan Ramadan, sukan fito a kan tituna suna murna tare da nuna alamu na shigar watan Ramadan mai alfarma.
Daga cikin al’adunsu a daren watanramadan sukan kunna wasu fitilu na usamman wadanda suke nuni da watan Ramadan, da kuma yawaita bayar da kyautuka da ciyar da marassa galihu da abinci a ko’ina a lokacin buda buda baki, amma shekarar bana lamarin ya canja saboda corona.