IQNA

23:01 - May 31, 2020
Lambar Labari: 3484851
Tehran (IQNA) da Asubahin yau ne aka bude Masallacin Manzon dake birnin Na Madina ga masallata, bayan kwashe watanni biyu a rufe saboda bullar cutar Annoba Korona.

Da Asubahin yau ne aka bude Masallacin Manzon dake birnin Na Madina ga masallata, bayan kwashe watanni biyu a rufe saboda bullar cutar Annoba Korona Virus, sai dai masallacin ne kawai aka bude amma Rauda za ta ci gaba da kasancewa a rufe, Kuma an bude masallacin ne tare da kula da mataken kare kai na lafiya,

Shi dai masallacin na Manzo da na na Haramin Makka an rufe su ne watanni biyu da suka gabata bayan bullar Annobar cutat Korona Virus, inda aka hana masallata gudanar da ibada a cikinsu, bisa kididdigar baya bayan nan Ma’aikatar lafiya ta kasar Saduiyya ta fitar ya nuna cewa kimanin mutane dubu 83 da 384 ne suka kamu da cutar yayin da 480 daga cikinsu suka rigamu gidan gaskiya .

 

3902087

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Madina ، masallacin ، manzon Allah ، mutane ، salla ، masallata
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: