IQNA

Musulmin Kasar Uganda Sun Kammala Azumin Shida Na Shawwal

23:06 - June 01, 2020
Lambar Labari: 3484853
Tehran (IQNA) musulmin kasar Uganda sun kammala azumin da suke yi na shiga a cikin watan shawwal.

Bisa ga rahoton kamfanin dillancin labaran iqna daga kasar Uganda, musulmin kasar suna gudanar da azumi shida bisa al’ada da zaran an kammala azumin watan Ramadan, wanda yake a matsayin azumin mustahabbi bayan na farilla da aka gudanar a cikin watan ramadaa.

Wannan dai wani lamari ne da musulmin kasdar Uganda suka jima suna gidanarwa domin samun ladar da take tattare da azumin kwanaki shida a cikin watan Shawwala, wato watan karamar salla kenan.

Ya zo a cikin hadisai da aka ruwaito kan falala da lada mai tarin yawa da take cikin wananna zumi na mustahabbi, wanda kuma bisa kwadayin wannan ladar ce muuslmia  ko’ina suka azumci kwanaki shida na shawwal.

Duk da cewa akwai maganganun malamai kan yadda za a azumci wadannan kwanaki shida a cikin shawwal, amma abin da yake da muhimamnci dai shi ne yin azumin a cikin kwanki 6 a tsakanin kwanaki talatin ko ashirin da tara da suke cikin watan.

 

3902452

 

captcha