IQNA

An Ci Gaba Da Gudanar Da Karatn Kur'ani A Gaza

23:50 - June 13, 2020
Lambar Labari: 3484891
Tehran (IQNA) yara sun ci gaba da gudanar da karatun kur'ani a cibiyoyin kur'ani na Gaza.

Shafin yada labarai na Bawwaba News ya bayar da rahoton cewa, daga yau Asabar yara sun ci gaba da gudanar da karatun kur'ani a cibiyoyin kur'ani na Gaza da sauran yankuna da ke yankin.

Bayanin ya ce an ci gaba da karatun bayan da katar da ajujuwan kur'ani na tsawon watanni uku, saboda bullar cutar corona.

Amma a halin yanzu saboda an samu sauki an ci gaba da karatu, sai dai tare da iyaye kaidoji an kiwon lafiya a dkkanin wuraren karatun.

A halin yanzu dai an fara karatun ne a cikin masallatai, ta yadda yara za su iya taruwa su yi karatun da aka yi mus baya domin tuni.

Wasu daga malaman kur'ani suna halartar masalatan domin su taimaka wa yara, musamman ma masu hardar kur'ani da kuma masu tilawa.

 

3904481

 

captcha