IQNA

Karatun Kur’ani Na Mutawalli Abdul Al A Birnin Tabriz

23:52 - July 09, 2020
Lambar Labari: 3484968
Tehran (IQNA) karatun kur’ani na marigayi Mutawalli Abdul Al shekaru 20 da suka gabata a birnin Tabriz na kasar Iran.

Tsohon hoton bidiyo na karatun kur’ani na marigayi Mutawalli Abdul Al shekaru ashirin da suka gabata a birnin Tabriz a shekarar 2000 tare da halartar masoya kur’ani, inda ya karanta surat Nasr.

An haifi Sayyid Matawalli a ranar 26 ga watan Afirilun 1947 a gidan malamai a kasar Masar, ya hardace kur’ani tun yana shekaru 12 da haihuwa, kuma ya fara karatu a bainar jama’a yana shekaru sha uku.

Ya kasance yana da salon karatunsa na musamman da aka san shi da shi, kamar yadda kuma yana koyi a wasu lokuta da manyan malaman kur’ani, kamar su sheikh Abdulbasit Abdulsamad da Sheikh Mustafa Isma’il.

Haka nan kuma ya kasance malami mai kouay da ilimin kur’ani da hukunce-hukuncen karatunsa, inda ya tarbiyantar da dalibai da dama.

Ya rasu a ranar 16 ga watan Yuli na shekara ta 2015.

 

3909394

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hardace ، Mutawalli Abdul Al ، masar ، Abdulbasit Abdulsamad ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha