IQNA

Jagororin Hamas Da Fatah Za Su Nan Ba Da Jimawa Ba

23:36 - July 23, 2020
Lambar Labari: 3485011
Tehran (IQNA) kakakin kungiyar Hamas ya sanar da cewa nan ba da jimawa shugabannin Hamas da Fatah za su hadu domin tattaunawa.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahton cewa, Hazim Kasim kakakin kungiyar Hamas ya sanar da cewa nan ba da jimawa shugabannin Hamas da Fatah za su hadu domin tattaunawa kan batutuwa da suka shafi lamarin al’ummar Falastinu.

Ya ce wannan ganawa tana da matukar muhimmanci, musamman a  cikin wannan lokaci da al’ummar Falastinu ke fuskantar shrin kawo karshen Falastinu baki daya.

Dangane da batun shrin Isra’ila na hade yanknan gabar yamma da kogin Jordan, ya bayyana cewa wannan shiri ne wanda yake da alaka da kawo karshen duk wani batu na kafa kasar Falstinu mai cin gishin kanta.

A farkon wannan wata na Yuli ne dai fira ministan Isra’ila ya shirya cewa zai hade yankunan falastinawa da ke yammacin kogin Jordan da sauran yankunan da Isra’ila ta mamaye, amma lamarin ya fuskanci kakkausar suka da rashin amincewa dag dukkanin kasashen duniya.

 

3912162

 

 

 

captcha