IQNA

Ayyukan Hajjin Bana A Karkashin Matakan kariya Daga Corona

22:22 - July 29, 2020
Lambar Labari: 3485034
Tehran (IQNA) An fara gudanar da ayyukan hajjin bana a yau a Makka tare da halartar alhazan da aka yarje mawa da su gudanar da aikin hajjin, wadanda aka takaita adadinsu.

Mahajjatan sun yi dawaful qudum, daga nan kuma sun yi sa’ayi tsakanin safa da Marwa, daga nan kuam suka nufi Mina domin yaum Tarwiyah, inda kuma a gobe ne za a yi tsayuwar arafah.

Kafin wannan lokacin dai mahukuntan Saudiyya sun sanar da cewa mutane 1000 ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana, kuma dukkaninsu daga cikin kasar, da suka hada da ‘yan kasa da kuma baki mazauna kasar.

Amma daga bisani kuma sun sanar da cewa mutane 10,000 ne za su gudanar da aikin hajjin, kashi talatin daga cikinsu jami’an kiwon lafiya ne, kamar yadda kuma dukkanin wadanda yarjewa gudanar da aikin hajjin sun cika sharuddan da aka gindaya, daga ciki har da gudanar da gwaji a kansu tare da tabbatar da cewa ba su dauke da cutar corona.

Haka nan kuma daga cikin sharuddan har da kebance kai kafin zuwa Makka, da kuma bayan zuwa Makka, gami da sake gudanar da gwaji, haka nan kuma shekarunsu su kasance tsakanin ashirin da biyar zuwa hamsin. 

حج 1441 در سایه کرونا با دستبند هوشمند و سنگ‌ریزه‌های ضدعفونی شده

فردا// حج 1441 در سایه کرونا با دستبند هوشمند و سنگ‌ریزه‌های ضدعفونی شده// گزارش

3913149

Abubuwan Da Ya Shafa: hajjin bana ، makka ، gudanar ، yarjewa ، gindaya ، kiwon lafiya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha