IQNA

22:43 - August 12, 2020
Lambar Labari: 3485078
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar China ta bayar da tallafin rage radadin cutar corona ga al’ummar kasar Saliyo.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, Hu Zhangliang jakadan kasar China a Saliyo ya bayyana cewa, wannan talafi ya zo ne domin kara karfafa alaka da ke tsakanin al’ummar China da kuma al’ummar Saliyo.

Wanann tallafi dai ya hada har da takunkumin rufe fuska guda dubu 10, da kuma wasu daga cikin kayayyakin kariya, gami da abinci da ya hada da shinkafa da kuma man girki.

Bayandu Dassama minsiatn kyautata rayuwar jama’a da jin dadinsu a kasar saliyo ya bayyana cewa, za su mika wannan taimako ga mutanen ad suka cancanta a kasar.

Kasar Saliyo da ke yammacin Afirka, kimanin kashi 78 na al’ummar kasar miliyan 7.65 musulmi ne.

 

3916157

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Saliyo ، bayyana ، dadinsu ، shinkafa ، takunkumin rufe fuska ، man girki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: