IQNA

An Yi Allawadai Da Kulla Alaka Tsakanin UAE Da Isra'ila

22:46 - August 14, 2020
Lambar Labari: 3485084
Tehran (IQNA) an yi Allawadai da kakausar murya kan kulla alaka tsakanin UAE da kuma gwamnatin yahudawan Isra'ila.

Cibiyar goyon bayan gwagwarmayan intifada ta al-ummar Falasdinu a majalisar dokokin kasar Iran ta yi allawadai da maida huldar jakadancin tsakanin kasar Hadaddiyar daular Larabawa da haramtacciyar kasar Isra’ila.

Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta ta nakalto ofishin yana fadar haka a safiyar yau Jumma’a a wani bayanin da ta fiyar.

Bayanin ya kuma kara da cewa kasar Falasdinu ta Falasdinawa ‘yan asalin kasar ne, wadanda suka hada da musulmansu masu rinjaye da kuma kiristoci da yahudawa.

Daga Karshe bayanin ya kara da cewa kaskancin da Abudhabi ta dauka ba zai cutar da gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi don dawo da kasarsu da aka mamaye ba.

A wani labarin kuma Kakakin majalisar dokokin kasar  ya yi allawadai da kaskacin da Hadaddiyar daular larabawa ta dauka na maida hulda da Isra'ila.

A jiya Alhamis ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan maida huldar jakadanci tsakanin Hadaddiyar daular Larabawa da kuma Isra'ila a kokarin da shugaban yake na neman yardar yahudawan Sahyoniyya kafin zaballawadaiubbukan Amurka a karshen wannan shekara.

 

3916468

 

captcha