IQNA

14:46 - August 18, 2020
1
Lambar Labari: 3485097
Tehran (IQNA) Allah ya yi wa babban sakataren kwamitin kusanto da mazhabobin muslucni na duniya Ayatollah Taskhiri rasuwa.

Ayatollah Muhammad Taskhiri ya kasance babban mai bawai jagoran juyin juya halin muslunci na Iran shawara kan harkokin duniyar musulmi, kuma shugaban baban kwamitin kusanto da mazhabobin muslunci na duniya, wanda ya rasu a yau yana da shekaru 76 a duniya.

Ayatollah Taskhiri ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada ilimin addini, da kuma kokarin hada kan al’ummar musulmi, ya kasance babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya tsawon shekaru masu yawa, saboda kwarewarsa  acikin harsunan larabci da kuma tirancin Ingilishi.

Baya ga haka kuma ya kasance mamba na babban kwamitin malaman addinin muslunci na duniya, amma ya fita daga kwamitin sakamakon wasu matakai da shugaban Kwamitin Sheikh Yusuf Qardawi ya rika dauka na siyasa.

 

3917335

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Aisha Imam
0
0
Allah ya jikan sa da rahamah
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: