Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a yau an kai wa wasu mata biyu musulmi da suke sanye ad lullubi hari da wukake a cikin birnin Paris fadar mulkin kasar faramsa.
Cibiyar da ke sanya ido kan kare hakkokin musulmia nahaiyr turai ta bayyana wannan harin da cewa na ta’addanci ne, kuma daidai yake da duk wani hari da ake kira na ta’addanci ba tare da laakari da wane ne ya kaddamar da harin ba.
Wannan cibiya ta bayyana cewa, kin jinin musulmi a kasar faransa ya karu matuka, wanda kuma ba daidai ba ne a dora karan tsana akan dukkanin musulmi a kasar, domin kuwa abin da ake fakewa da shi na ayyukan masu tsatsauran ra’ayi daga cikin musulmi, ko musulmi ba su tsira ba.
A kan haka bayanin y ace dole mahukunta akasar ta faransa su dauki matakai na ganin sun kare musulmi kamar yadda ake kare kowane dan kasa, domin su ma ‘yan kasa da suke da ahkkoki kamar kowa, kuma dole ne a kare musu hakkokinsu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
3930680