IQNA

23:35 - October 23, 2020
Lambar Labari: 3485301

Fiye Da Masallata Dubu 20 Ne Suka Yi Sallar Juma’a A Yau A Masallacin Aqsa

Tehran (IQNA) fiye da masallata dubu 20 ne suka gudanar da sallar juma’a a yau a masallacin Aqsa.

Fiye Da Masallata Dubu 20 Ne Suka Yi Sallar Juma’a A Yau A Masallacin Aqsa

Shafin yada labarai na Palestine ya bayar da rahoton cewa, a yau a masallacin Aqsa mai alfarma, fiye da masallata dubu 20 ne suka gudanar da sallar juma’a.

Wannan kuwa na zuwa ne duk da irin matakan da jami’an tsaron gwamnatin yahudawan Isra’ila suka dauka na takura masallatan, inda suke tantance dukkanin masu shiga cikin masallacin kafin shiga domin yin salla.

Sheikh Yusuf Abu Saninah, wanda ya jagorancin sallar Juma’a a yau a masallacin Aqsa, ya jaddada wajabcin hadin kai tsakanin dukkanin al’ummar Falastinu, da kuma mara baya ga fursunoni Falastinawa da Isra’ila take tsare da su.

3930897

 

captcha