IQNA

23:11 - October 26, 2020
Lambar Labari: 3485306
Tehran (IQNA) sakamakon cin zarafin manzon Allah (SAW) Macron na ci gaba da shan martani.

Sakamakon ci gaba da yin batunci ga manzon Allah (SAW) da ake yi a kasar Faransa, jama’a da dama a kasar Kuwait sun kaurace wa sayen kayayyakin kasar ta Faransa.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Kuwait ta fitar da wani bayani, wanda a cikinsa ta nuna bacin rai matuka dangane da yadda wasu jami’an gwamnatin kasar Faransa suka fitoa fili suna sukar addinin muslunci, tare da nuna goyon baya ga cin zarafin annabawan Allah.

Bayanin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya gargadi kasar Faransa kan yin sakaci da irin wannan lamari mai matukar hadari, wanda zai iya mayar da hannun agogo baya a kan dukkanin kokarin da ake yi tsakanin kasashen na hada kan al’ummomi domin samun zaman lafiya da fahimtar juna, da kuma girmama akidar kowa.

A wani rahoto da kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar an bayyana cewa, fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya dan kasar Faransa ya sanar da daina bugawa kungiyar kwallon kafa ta kasar Faransa wasanni, saboda kalaman batunci ga addinin da shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi.

Dan wasan kwallon kafa na duniya dan kasar Faransa da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wasanni Paul Pogba, ya sanar da dakatar da bugawa kungiyar kwallon kafa ta Faransa wasanni, saboda Emmanuel Macron ya kira addinin muslucni da addinin ta’addanci.

Pogb ya ce hakika ransa ya baci matuka a matsayinsa na musulmi, kan yadda shugaban kasar Faransa Macron ya danganta ta’addanci da addinin muslunci.

Ya kara da cewa, baya ga kalaman batunci ga addinin muslunci da Macron ya yi, ya kuma fito fili yana goyon bayan abin da malamin makaranta ya yi, na nuna zanen batunci da cin zarafin ga manzon Allah (SAW) wanda dukkanin wadannan dalilan ne suka hadu suka sanya shi yanke shawar daina bugawa Faransa wasa.

 

 

3931251

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: batunci ، manzon allah ، bugawa ، malamin makaranta ، kasar Faransa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: