IQNA

Jerin Gwanon Neman Sakin Sheikh Zakzaky A Abuja

23:08 - November 25, 2020
Lambar Labari: 3485400
Tehran (IQNA) a ci gaba da kiran a saki sheikh Zakzaky da mai dakinsa magoya bayan Harka Islamiyya sun yi jerin gwanon lumana a Abuja.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, magoya bayan Harka Islamiyya a Najeriya sun gudanar da jerin gwano a birnin Abuja, na neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky da ake ci gaba da tsare shi tare da mai dakinsa Malama Zinat Ibrahim.

A shekara 2016 ne kotun tarayya a Abuja, ta bayar da umarnin sakin Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa har ma da biyansu diyya, saidai har yanzu ana ci gaba da tsare su.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama na ciki da wajen Najeriya sun yi ta yin irin wannan kira ga gwamnatin Najeriya, musamman ganin yadda yake fama da matsaloli na rashin lafiya.

A cikin makon da ya gabata ne kotun da ke sauraren shari’arsa ta sake dage zaman sauraren shari’ar har zuwa cikin shekara ta dubu biyu da ashirin da daya.

 

3937260

 

 

 

 

captcha