A cikin rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya harhada, ya kawo wasu abubuwa da suka farua da musulmi a wasu kasashe a cikin shekara ta 2020, musamman ma kasashen da musulmi suke marassa rinjaye.
1 – Bullar corona na daga cikin abubuwan da suka shafi duniya baki daya, amma kuma musulmi sun fuskanci matsaloli a wasu kasashe sakamakon hakan, inda aka rika takura su da sunan hana yaduwar cutar corona, wanda hakan yafi yawa a kasashen turai.
2 – Sakamakon matsalolin da musulmi suka fuskanta a hannun gwamnati da ta fadi zabe a kasar Amurka, wannan ya sanya fiye da kashi 95% na musulmin Amurka, sun jefa wa Joe Biden kuri’arsu, domin samun canjin siyasa a kasar, ta fuskar wariya da cin zarafin jama’a saboda addini ko kuma launin fada.
3 – Al’ummomin duniya da dama sun nuna damuwa kan halin da musulmin kasar China suka samu kansu na nuna musu fin karfi, da kuam tilasta su yin abin da ya saba wa addininsu, inda kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suka tashi tsaye wajen sukar wannan mataki na China a kan musulmin Igoir.
4 – A cikin wannan shekara ne aka kai Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran harkar musulunci a Najeriya asibitin kasar India sakamakon matsalolin da yake fama da su tare da maidakinsa malama Zinat, amma kuma bai samu biyan bukatarsa ba, kuma bayan dawowa da shi, an ci gaba da tsare a gidan kaso, inda har yanzu yanayin jikinsa da mai dakinsa ke bukatar kulawa ta musamman a cibiyoyi na kiwon lafiya, wanda kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama sun bukaci gwamnatin Najeriya da ta sake su domin samun magani.
5 – Ci gaba da karuwar ayyukan ta’addancin kungiyoyi masu da’awar jihadi a cikin kasashen musulmi, inda irin wadannan kungiyoyi masu dauke da tsatsaurar akidar wahabiyanci da suke kafirta musulmi, inda suke kashe musulmi da wanda ba musulmi ba da sunan jihadi, babban misali kan hakan shi ne abin da yake faruwa a kasar Afghanistan, Najeriya, Mali da Syria da makamantansu.
6 – Mawuyacin halin da musulmin kasar Myanmar da suke gudun hijira suke ciki a kasashen da aka tsugunnar da su, inda har yanzu da dama daga cikinsu suke cikin mawuyacin hali, duk da cewa majalisar dinkin duniya ta bayyana taimakon da take samu dmin taimaka musu ya kadan matuka, amma kasashen duniya ba su sauke nauyin da ya rataya kansu domin taimaka wadannan mutane, musamman ma kasashen musulmi masu tarin dukiya wadanda zasu iya daukar nauyinsu baki daya.
7 – A kasar Faransa a cikin wannan shekara gwamnatin kasar ta tsananta matakan da take dauka wajen takura musulmi, sakamakon yadda suka nuna rashin amincewarsu da cin zarafin manzon Allah (SAW) da jaridar kasar ke yi, wanda hakan ke samun goyon baya kai tsaye daga gwamnatin kasar.
8- Musulmi a kasar India sun nuna damuwa da rashin amincewa da sabuwar dokar da aka kafa kan samun izinin zama dan kasa a cikin wannan shekara wadda take nuna wariya musulmi.
Mahukuntan kasar India sun yi amfani da karfi domin murkushe duk wani yunkurin da musulmi suka yi domin kalublantar wannan doka ta hanyoyi daban-daban, daga cikin har da jerin gwano na lumana, amma jami’an tsaro da mabiya addinin Hindu sun fadawa musulmi tare da kashe su a wasu wuraren da kuma wawushe musu dukiyoyi.
9 – A wasu kasashe kuma an samu ci gaba ne ta fuskacin tsarin tattalin arziki da ajiya kudade a bankun musulunci.
Da dama daga cikin kasashe da suka karbi tsarin banki na musulunci sun nuna gamsuwa da yadda tsarin yake, da hakan ya hada da kasashe wadanda ba na musulmi ba musamman a nahiyar Afirka, da kuma wasu kasashen nahiyar Asia.
10 – A cikin wannan shekara ne kotun kasar New Zealand ta yanke hukuncin daurin rai da rai wanda babu afuwa a cikinsa a kan mutumin da ya bude wuta a kan musulmi a cikin masallaci, inda zai karar da rayuwarsa baki daya a cikin gidan kaso.
A ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata ne dai kotun kasar New Zealand ta yanke hukunin daurin rai da rai wanda babu afuwa a cikinsa a kan mutumin mai tsatsauran ra’ayin kin addinin musulunci dan kasar Australia, wanda ya kashe musulmi 51 tare da jikkata wasu 41 a cikin masallaci a kasar New Zealand, wanda kuma wannan shi ne karon farko da kotu ta yanke hukunci mai tsanani a tarihin kasar.