Babban kwamandan dakarun Hashd Al-shaabi a Iraki Faleh Fayyad ya bayyana cewa, nan da wani dan lokaci mai zuwa majalisar dokokin kasar Iraki za ta aiwatar da kudirin fitar da sojojin Amurka daga kasar baki daya.
A wata zantawa da tashar Amasirah, Faleh Fayyad ya jaddada cewa, babu gudu babu ja da baya dangane da batun ficewar sojojin Amurka daga Iraki, wanda kuma majalisar ta fitar da wannan kudiri ne sakamakon kisan Kasim Sulaimani da Abu Mahdi Al-Muhandis da Amurka ta yi a cikin kasar Iraki.
Ya ce wanann zai wakana nan da ‘yan kwanaki masu zuwa da yardar Allah, domin hakan shi ne kawai mafita kuma abin da ya dace da Amurka.
Dangane da alaka tsakanin Iran da Iraki kuwa, ya bayyana cewa alaka ce mai karfi, wadda babu abin da zai girgiza ta, kuma bangarorin biyu za su ci gaba da yin aiki tare a dukkanin bangarori.