IQNA

Sakon Jagora Na Ta’aziyyar Ayatollah Mesbah Yazdi:

Hidimar Da Ayatollah Mesbah Yazdi Wajen Yada Ilimin Addini Tana Girma

14:42 - January 02, 2021
Lambar Labari: 3485516
Tehran (IQNA) jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya aike da sakon ta’azziyar rasuwar Ayatollah Muhammad Mesbah Yazdi, daya daga cikin manyan malaman addini a Iran da Allah ya yi masa rasuwa a jiya.

Kamfanin dillancin laraban iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yau jagora Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya aike da sakon ta’azziyar rasuwar Ayatollah Muhammad Mesbah Yazdi.

Ga matanin sakon kamar haka:

 

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai

Na Samu labarin rasuwar babban malamin addinin muslunci mujahidin fakihi Ayatollah Muhammad Mesbah Yazdi.

Hakika wannan babbar asara ce ga babbar cibiyar ilimi ta hauza baki daya, domin an rasa wani mutum da ba kasafai a kan samu irinsa ba, ta fuskar iliminsa da kokarinsa na yada ilimi, da kuma samar da dalibai wadanda ya kan mayar da su manya malamai daga ilimin da Allah ya hore masa.

A bangaren kare juyin islama a kowane lokaci ya kasance a sahun gaba, kamar yadda kuma ya kasance mai tsantsene dad a tsoron Allah a cikin lamarinsa, kasantuwarsa a cikin mutane bababr kyauta ce ta Allah a gare su.

Kamar yadda nake cikin alhini na rashin babban aboki na tsawon shekaru masu yawa, haka nake isar da sakon ta’aziya ga iyalansa baki daya, da kuma cibiyar ilimi ta hauza da dukkanin malamanta, Allah ya gafarta masa ya yi masa rahma, ya daukaka darajarsa.

 

Sayyid Ali Khamenei

2 – 1 - 2021-01-02

 

3944863

 

 

captcha