IQNA

Cikakkiyar Tilawar Kur’ani Da Sautin Makarancin Kur’ani Mafi Karancin Shekaru A Morocco

20:49 - January 21, 2021
Lambar Labari: 3485574
Tehran (IQNA) Yahya Sidqi shi ne mafi karancin shekaru a tsakanin fitattun makarantan kur’ani a kasar Morocco.

Shafin yada labarai na Casa24 ya bayar da rahoton cewa, Yahya Sidqi  mafi karancin shekaru a tsakanin fitattun makaranta da mahardata  kur’ani a kasar Morocco, ya saka tilawar kur’ani mai tsarki da sautinsa a shafukan yanar gizo.

Yahya Sidqi wanda karamin yaro day a samu tarbiya ta kur’ani a gaban mahaifansa, yana daga cikin makaranta kur’ani mafi shahara  akasar Morocco a halin yanzu.

Baya ga karatun kur’ani a masallatai da kuma wurarn tarukan addini da yake gabatarwa, yana kuma halartar tarukan gasar kur’ani ta duniya a kasashe daban-daban.

Yahya yana da kakkyawan sautin karatun kur’ani mai tsarki, kamar yadda kuma yana da basira da yin amfani da salon a wasu fitattun makaranta, kamar su Sheikh Siddiq Minshawi, da Sheikh Khalil Al-Husari da makamantansu.

Yanzu haka dai a nau’oin karatuttukansa  a cikin shafinsa na facebook, wanda mutane fiye da dubu 43 suke bibiyarsa.

3948929

 

 

captcha