IQNA

Tilawar Anwar Shuhat Anwar A Kermanshah

22:32 - February 09, 2021
Lambar Labari: 3485635
Tehran (IQNA) Anwar Shuhat Anwar a yayin wata tilawa da ya yi a Husainiyar Kermansha a kasar Iran.

A cikin wannan hoton bidiyo Anwar Shuhat Anwar yana karatun kur’ani mai tsarki inda yake karanta wasu ayoyi masu albarka daga cikin surat Shams.

Anwar Shuhat Anwar an haife shi ne a ranar 29 ga watan Mayun 1979 a kasar Masar, mahaifinsa shi ne Shuhat Muhamad Anwar, dan uwansa kuma shi ne Mahmud Shuhat Anwar, wadanda dukkaninsu fitattun makaranta kur’ani ne a kasar Masar da ma duniya.

Anwar Shuhat Anwar ya yi tafiye zuwa kasashen duniya da ake gayyatarsa domin gabatar da karatun kur’ani mai tsarki, daga cikin kasashen akwai Burtaniya, Iran, Pakistan, Indonesia, Afirka ta kudu, Aljeriya da sauransu.

3953016

 

 

 

 

 

 

 

captcha