IQNA

Tashar Al-ahad Ta Iraki:

Sakamakon Binciken Iran Dangane Da Kisan Manyan Kwamandoji Ya Isa Hannun Gwamnatin Iraki

22:37 - February 09, 2021
Lambar Labari: 3485636
Tehran (IQNA) alkalin alkalan Iran ya bayyana cewa Tabbas za a dauki fansar kisan da Amurka ta yi wa manyan kwamandojin gwagwarmaya.

Alkalin alkalan Iran Ibrahim Ra’isi wanda ya isa birnin Bagadaza domin ziyarar aiki ne bayyana cewa; Tabbas za a dauki fansar kisan da Amurka ta yi wa Kasim Sulaimani da Abu Mahdi al-Muhandis.

Ra’isi ya ziyarci wurin da kwamandojin biyu su ka yi shahada a kusa da filin saukar jiragen sama na Bagadaza, inda ya bayyana yadda Amurka ta yi furuci da kirkirar kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Shugaban ma’aikatar shari’ar ta Iran ya kuma kara da cewa; Shahidan biyu suna a matsayin manyan alami ne na daukaka da karfin da al’ummar musulmi su ke da su, kuma za su ci gaba da zama a matsayin hakan har abada.

Ra’isi ya kuma jinjinawa al’ummar Iraki, inda ya bayyana cewa; suna tafiya ne akan tafarki daya na gwgawarmaya.

Ziyarar da Ibrahim Ra’isy tana a matsayin amsa kira ne na shugaban hukumar shari’a ta kasar Iraki.

3953230

 

 

 

 

 

 

 

captcha