A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan cikar shekaru 42 da yau juyin juya halin muslunci na kasar Iran, kafofin yada labarai da dama na duniya sun mayar da hankali a kan yadda bukukuwan ke gudana a yau.
Tashar Aljazeera na daga cikin kafofin yada labarai na yankin gabas ta tsakiya da suka mayar da hankali kan wannan rana wadda tun a safiyar yau wakilanta suke gudanar da ayyukan daukar rahotanni a cikin birnin Tehran da kewaye.
Baya ga haka kuma wasu daga cikin kafofin yada labaran yankin, tashar Almayadeen daya daga cikin fitattun tashoshin larabawa da ke watsa shirinta daga kasar Lebanaon, a yau ta mayar da labarin cikar shekaru 42 da samun nasarar juyin juya halin muslunci a Iran ya zama daga cikin muhimman labaranta.
Baya ga tashoshin larabawa da sauran kafofin yada labarai na yankin gabas ta tsakiya, wasu daga cikin muhimman kafofin yada labarai na duniya, da suka hada da kamfanin dillancin labaran Associated Pres, da kuma Reuters, gami da Agency of France Press, duk sun dauki wannan labari.
Haka nan kuma manyan tashohi da kamfanonin dllancin labarai na kasar Rasha, da suka hada da tashar RT, gami da kamfanin dillancin labarai na sputnik da iterfax da sauransu, duk sun dauki wannan labari a cikin manyan labaransu na yau.