IQNA

Masallacin New York Na Daga Cikin Muhimman Wuraren Tarukan Musulmin Amurka

23:39 - February 16, 2021
Lambar Labari: 3485657
Tehran (IQNA) ginin masallaci da cibiyar musulunci da ke birnin New York na kasar Amurka na daga cikin muhimman wuraren tarukan musulmin Amurka.

Babban ginin masallaci da cibiyar musulunci da ke birnin New York na kasar Amurka na daga cikin muhimman wurare da musulmin kasar Amurka suke gudanar da tarukansu.

An gabatar da tsarin yadda za a gina wannan masallaci da cibiya ne tun fiye da shekaru hamsin da suka gabata, amma saboda tattara kudaden da za a yi amfani da su domin gudanar da aikin ginin, amma a karshen watan Oktoban 1984 ne aka fara aikin gina cibiyar.

A cikin watan Mayu shekara ta 1987 ne aka fara gina bangaren masallaci a wannan cibiya, a rana 15 ga watan Afirilun 1991 kuma aka kammala aikin, kuma aka bude wurin a ranar sallar idin Fitr.

An gina wannan wuri ne ta yadda zai iya daukar masala 1000, haka nan kuma an kashe kudi kimanin dala miliyan 14.

Baya ga salla, ana gudanar da karatun addini da kuma sauran tarukun musulunci, haka nan kuma ana yin taron daurin aure da kuma tarukan ta’aziyya.

مسجد و مرکز اسلامی نیویورک: از ایده در دهه شصت تا ساخت در دهه نود+ فیلم

3953899

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha