IQNA

23:41 - March 04, 2021
Lambar Labari: 3485711
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen kasar Iran ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwan Allamah Ahmad Zain babba malamin Ahlussunna a Lebanon.

A cikin sakon ta’aziyyar da ministan harkokin wajen na Iran ya aike ga kungiyar malaman addinin musulunci ta kasar Lebanon, ya bayyana malamin da cewa ya taka rawa matuka a fagen samar da hadin kan al’ummar musulmi, sunna da shi’a a lokacin da yake raye, ba a cikin Lebanon ba kadai, har da duniyar musulmi baki daya.

Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya yaba da matsayar marigayin a fagen gwagwarmaya da ‘yan sahayoniya da jajurcewarsa a kan wajabcin ‘yanto da Palasdinu.

Gabanin rasuwarsa, Sheikh Ahmad Zain ya kasance daya daga cikin fitattun malaman Ahlussunah a Lebanon, kuma ya taba zama alkali a garin Saidha, sannan kuma shugaban majalisar malaman addinin musulunci a kasar.

Allamah Ahmad Zain ya kasance babban misali na malamai masu kokarin hada kan al’ummar musulmi, kamar yadda kuma ya kasance a sahun gaba wajen goyon bayan al’ummar Falastinu, da adawa da zaluncin da Isra’ila take yi a kansu.

 

3957320

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: