IQNA

‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kashe Sojojin Nijar Hudu

20:04 - April 05, 2021
Lambar Labari: 3485786
Tehran (IQNA) ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin jamhuriyar Nijar guda 4 tare da jikkata wasu.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da rundunar sojin kasar Nijar ta fitar a jiya, ta bayyana cewa mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram ta kaddamar da haria  yankin Diffa da ke kudu maso gabashin jamhuriyar Nijar.

A bias wannan bayani na rundunar sojin Nijar, ‘yan ta’addan na kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin jamhuriyar Nijar guda 4 tare da jikkata wasu 3 a yayin wannan hari.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, yan ta’addan sun yi amfani da manyan bindigogi da makamai masu hadari yayin kaddamar da harin.

‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram dai sun addabi al’ummomin kasashen Najeriya da Nijar gami da Kamaru da Chadi, amma a baya-bayan nan dai sun tsananta hare-haren nasu a cikin Najeriya da Nijar.

Tun a cikin shekara ta 2002 ce dai aka kafa kungiyar Boko Haram a Najeriya, wadda take dauke da akidar Salafiyyah wahabiyyah, daga nan kuma ta shelanta jihadi kan al’ummar Najeriya bayan kafirta su.

3962515

 

captcha