IQNA

Najeriya: Mayakan Boko Haram Sun Mamaye Wasu Yankunan Jihar Neja 

14:35 - April 28, 2021
Lambar Labari: 3485855
Tehran (IQNA) Boko Haram ta mamaye kananan hukumomin Kaure da Shiroro dake jihar Neja a Najeriya.

Gwamnan jihar Abubakar Bello ya bayyana cewa Boko Haram ta mamaye kananan hukumomin Kaure da Shiroro dake jihar, baya ga haka kuma sun kwace wa magidanta matayensu sun rabawa kansu, sannan sun kafa tuta a tsakiyar Garuruwan.

A rahoton da jaridar Premium Times ta bayar, ta bayyana cewa hakan  ya zo ne a cikin sanarwar da babban mai bai wa gwamna Bello shawara kan watsa labarai Mu’awuya Muye ya fitar, inda ya ce gwamnan ya bayyana cewa: “Boko Haram sun kwace yankin sun kuma kafa tutarsu, ina tabbatar da hakan a yanzu”

Gwamna Bello ya ce, ya dade ya na kwankwasa kofar fadar gwamnatin tarayya a Abuja domin ya kai kukansa kan kwararowar Boko Haram jiharsa domin a gaggauta daukar mataki a kan hakan, amma ba a yi komai ba, to yanzu abin tsoron shi ne ita kanta  Abuja ba za ta tsira ba.

Domin a cewar gwamnan, Sambisa na da nisa daga Abuja, amma Kaure kusa ta ke da Abuja, saboda haka a halin yanzu babu wanda zai kubutar da Abuja daga kwararowarsu.

Gwamnan na jihar Neja ya ce shi a halin yanzu ya gama sauraren wani kan batun tsaron jiharsa, zai dauki matakin da yake ganin ya dace ne kawai kai tsaye.

 

3967708

 

captcha