Tehran (IQNA) wasu 'yan bindiga sun kashe wani limamin musulmi a kasar Congo ta hanyar harbinsa da bindiga.

Kamfanin dillancin labaran sky News Arabic ya bayar da rahoton cewa, wasu yan bindiga da ba san ko su wane ne ba sun kashe Sheikh Ali Amin wani limamin musulmi a kasar Congo, a lokacin da yake bayar da sallar Isha'i a masalaci.
Sheikh Amin dai ya shahara da nuna adawa da duk wani tunani na tatsauran ra'ayi ko ta'addanci da sunan addini.
Ko a cikin watan Nuwamban shekara ta 2019 wasu masu tsatsauran ra'ayi da suke da makamai sun kai wasu munanan hare-haren yankin da yake inda suka kashe mutane.
A daren jiya ma mayakan da suke dauke da makamai da ake zargin suna da alaka da kungiyar Daesh sun kai hare-hare sun kashe mutane da hakan ya hada da shi kansa limamin.