IQNA

Falastinawa 122 Ne Suka Yi Shahada A Zirin Gaza Cikin Kwanaki Hudu

21:13 - May 14, 2021
Lambar Labari: 3485914
Tehran (IQNA) Falastinawa 122 ne suka yi shahada a yankin zirin Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila a kan yankin.

A cikin kwanaki hudu da gwamnatin yahudawan Isra'ila ta kwashe tana kaddamar da hare-hare a kan al'ummar yankin zirin Gaza da ke falastinu, ya zuwa Juma'a Falastinawa 122 ne suka yi shahada sakamakon wadannan hare-hare.

Rahotannin sun tabbatar da cewa, daga cikin wadanda suka yi shahada 31 kananan yara ne, sai kuma 11, yayin wasu daruruwa kuma suka samu raunuka.

Baya ga haka kuma a yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, a cikin kwanaki hudu ya zuwa yau, Falastinawa 9 ne suka yi shahada.

Duk da hakan a nasu bangaren Falastinawa 'yan gwagwarmaya daga Gaza suna mayar da martani da makaman roka da kuma masu linzami.

Majiyoyin gwamnatin yahudawan sun tabbatar da cewa a yau Hamas ta harba wani jirgi maras matuki ya kuma ragargaza wani rumbu na sanadarai masu guba a Israila, wanda kuma ya rusa wasu injinun samar da wutar lantarki a ga wasu matsugunnan yahudawa.

 

 

3971517

 

 

captcha