IQNA

Isra'ila Ta Rusa Babban Ginin Da Kafofin Yada Labarai Na Duniya Suke Amfani Da Shi A Gaza

23:53 - May 15, 2021
Lambar Labari: 3485917
Tehran (IQNA) Isra’ila ta rusa wani ginin da kafofin yada labarai suke amfani da shi a Gaza,

Sojojin Isra’ila, sun rusa wani ginin da kafofin yada labarai suke amfani da shi a Gaza, daga cikin kafofin kuwa har da tashar talabijin ta Aljazeera mallakin Qatar da kuma kamfanin dilancin labaren AP.
Ginin mai hawa 13 wanda ya kushi ofosohin ‘yan jarida da dama an rusa shi ne ta hanyar harin jiragen sama jim kadan bayan sanar da mai ginin cewa kowa ya yi ta kan shi.
Shugaban kamfanin dillancin labaran na AP, ya fitar da wata sanarawa inda ya sun tsorata da kuma jin mamaki da matakin na Isra’ila
Ita kuwa tashar Aljazeera tir ta yi da harin, tana mai cewa hakan ba zai sanya ta yi shiru ba game bayana abubuwan da ke faruwa a yankin.
Daga bisani dai an ruwaito sojojin Isra’ila na cewa, sun kai harin ne saboda ana ajiye kayan soji a ciki.

3971683

 

 

 

 

 

captcha