IQNA

Tehran (IQNA) a yau jiragen yakin yahudawan Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a kan al'ummar Gaza.

Jiragen yakin yahudawan Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a kan al'ummar Gaza, tare da kashe adadi mai yawa na Falastinawa, inda adadin mutanen da suka yi shahada a cikin kwanakin nan ya kai 139 da suka hada yara 39 da mata 22.