IQNA

Netanyahu: Za Mu Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Al'ummar Gaza Har Nan Da Wasu Kwanaki

22:55 - May 18, 2021
Lambar Labari: 3485928
Tehran (IQNA) Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za su ci gaba da kai hare-hare kan al'ummar Gaza har nan da wasu kwanaki.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za su ci gaba da kai hare-hare kan al'ummar zirin Gaza har nan da wasu kwanaki masu zuwa.

Jaridar Times ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da Netanyahu yake ganawa da wasu daga cikin magaddan gari daga wasu yankunan kudancin Falastinu da Isra'ila ta mamaye, ya bayyana cewa za su ci gaba da kai hare-hare kan al'ummar zirin Gaza har nan da wasu kwanaki masu zuwa., bayan nan kuma duk wani da za a kai kansu za su mayar da martani mai tsanani.

Tun bayan da aka kafa haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kasar Falastinu, ba ta taba fuskantar turjiyar da ta fuskanta da hare-haren ramuwar gayya kamar irin wannan lokacin ba.

Duk da kisan Falastinawa kananan yara da mata da tsoffi da sauran fararen hula da Isra'ila take yia  Gaza, amma a wannan karon lamarin ya sha banbam da sauran shekarun baya, domin a wannan karon ta fuskanci martani da makamai masu linzami sama da dubu uku a cikin kasa da mako guda daga Falastinawa.

Hare-haren martanin na Falastinawa ya jawowa Isra'ila asarori masu tarin yawa na tattalin arziki, baya ga halakar wasu yahudawa da suka hada har da jami'an tsaronta, baya ga haka kuma a wanann karon dukkanin yankunan Falastinawa ne talke fuskantar turjiya ba a Gaza ba kawai, ida koa  yau Lahadi a cikin yankunan gabar yamma da kogin Joradan, Falastinawa sun halaka wasu yahudawa biyu ta hanyar harbe su da bindiga a musayar wuta da suka yi da su.

 

3972368

 

captcha