IQNA

An Sake Kashe Wani Limamin Musulmi  A Gabashin Kasar Congo

19:11 - May 20, 2021
Lambar Labari: 3485934
Tehran (IQNA) An harbe wani limamin musulmi a yankin gabashin kasar Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

Shafin yada labarai na Ilaf ya bayar da rahoton cewa, a daren Talata da ta gabata, wani mutum dauke da bindiga ya harbe Sheikh Musa Jamali limamin masulmi a yankin gabashin kasar Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

Rahoton ya ce, Donat Kivana shugana lardin gabashin Congo ya bayyana cewa, bisa ga rahoton da suka samu wani mutum ne dauke da bindiga ya harbe Sheikh Musa Jamali bayan ya fito daga masallaci, bayan kammala sallar Isha’i, kuma mutumin ya tsere kafin mutane su an kara.

Ya ce tuni jami’an tsaro suka shiga gudanar da bincike kan lamarin, inda ya ce babu wani mutum ko wata kungiya da suka dauki alhakin kai harin, amma dai ana zargin kugiyar Jama’at Islamiyya, wata kungiyar ‘yan Salafiyya masu tsatsauran ra’ayi da ke da’awar Jihadi a yankin.

Ko a  farkon wannan wata na Mayu ‘yan wannan kungiya sun kashe Sheikh Ali Amini, daya daga cikin jagororin musulmi na kasar Congo da ke zaune a  yankin, wanda shi ma sun kashe shi ne bayan fitowarsa daga masallaci bayan kammala sallar isha’i.

Tuni dai gwamnatin Congo ta haramta wannan kungiya ta Jama’at Islamiyya, ta ‘yan salafiyya masu tsatsauran ra’ayi da ke da’awar jihadi da kuma kafirta sauran musulmin kasar.

3972675

 

captcha