Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayaninsa a gaban manema labarai, Firayi ministan kasar Burtaniya Boris Johnson ya bayyana nadama kan yin kalaman batunci da rika yi a kan addinin muslunci.
A cikin sheakara ta 2018, Boris Johnson ya yi wasu kalamai na batunci da cin zarafi ga addinin muslunci, daga ciki har da cewa, mata musulmi masu saka burqa, sun yi kama da akwatin saka wasiku, kuma sun yi kama da barayi masu fashi a bankuna.
Boris Johson ya ce ya yi wadannan kalamai ne a lokacin yakin neman zabe, amma yanzu ya fahimci cewa ya yi amfani da lafazi na batunci a cikin kalaman nasa, wanda idan da yanzu ne da yake rike da mukamin Firayi minista ba zai taba yin irin wadannan kalaman ba, saboda haka ya yi nadamar hakan, yana kuma bayar da hakuri.
Sai dai a nata bangaren kungiyar da yaki da akidar nuna wariya a kasar Burtaniya ta Hope not hate, ta bayyana neman uzurin da Johnson ya yi kan kalamansa na batunci ga addinin musulunci da cewa hakan bai wadatar ba.
Babban daraktan kungiyar Nick Luis ya bayyana cewa, wannan ba magana ce ta neman uzuri ba kawai, magana ce ta daukar mataki a aikace, wajen kawo karshen wariya da kin jini da ake nuna wa musulmi, ko wani jinsin mutane saboda akidarsu ko addininsu a kasar Burtaniya.