IQNA

Landan: Wasu Daga Cikin Malaman Yahudawa Sun Yi Allawadai Da Zaluntar Musulmi Da Wasu Yahudawan Ke Yi

23:00 - May 29, 2021
Lambar Labari: 3485961
Tehran (IQNA) Wasu daga cikin manyan malaman yahudawan Burtaniya sun fitar da bayanin da ke yin Allawadai da duk wani cin zarafi a kan musulmi da wasu yahudawan ke yi.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin manyan malaman yahudawa a birnin Landan na kasar Burtaniya, sun fitar da bayanin da ke yin Allawadai da duk wani cin zarafin musulmi da yahudawan sahyuniya ke yi a fadin duniya.

Bayanin malaman yahudawan ya ce, abin ban takaici ne yadda wasu masu dawa’ar cewa suna bin addinin yahudanci da aka saukar daga sama, suke cutar bil adama, wanda hakan a  cewar bayanin, ba koyarwar addinai da Allah ya saukar ba ne.

Manyan malaman yahudawa 14 ne suka rattaba hannu a kan bayanin a birnin Landan, inda suka jaddada cewa, duk wani bayahuden da ya cutar da musulmi, to baya wakiltarsu a matsayinsu na masu bin koyarwar addininsu.

Bayanin ya ce, yahudawan Arthodox, sun yi imanin cewa, addininsu addinin zaman lafiya ne da kowa, sabanin abin da yahudawan sahyuniya suka yi imani da shi.

Daga karshe sun jaddada cewa suna kara yin Allawadai da cutar da musulmi da yahudawan sahyuniya suke yi, saboda a cewarsu idan ba su Allawadai da hakan ba, to Allah zai yi fushi da su.

Musulmi a Falastinu da kasashen larabawa da ma sauran kasashen duniya sun yi lale marhabin da wannan matsaya ta manyan malaman yahudawa a Lanadan.

3974218

 

captcha