IQNA

Netanyahu Ya Kama Hanyar Shiga Kwandon Shara A Siyasar Isra’ila

22:48 - June 03, 2021
Lambar Labari: 3485981
Thran (IQNA) bayan da Netanyahu ya kasa kafa gwamnatin yahudawan Isra’ila, abokan hamayyarsa sun yi nasara wajen sanar da kafa gwamnati.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, jagoran adawa a Isra'ila Yaïr Lapid ya bayyana samun nasarar kulla kawancen jam'iyyun siyasar da ka iya bashi damar kafa sabuwar gwamnati da za ta maye gurbin Firaminista Benjamin Netanyahu daga karagar mulki.

Da zaran Majalisar dokoki ta tabbatar da adadin yawan Yan Majalisun da suka goyi bayan wannan sabon kawancen, matakin zai kawo karshen mulkin shekaru 12 na Firaminista Netanyahu wanda ke fuskantar zargin almundahana da cin hanci da rashawa.

 

A karkashin wannan sabon kawancen, Naftali Bennett mai shekaru 49 zai zama Firaminista na farko a yarjejeniyar da za’a dinga musayar mukamin, yayin da Lapid zai karbi kujerar bayan shekaru 2.

Ana saran nan da mako guda Majalisar dokokin Israila ta kada kuri’ar amincewa da sabon kawancen abinda zai bata damar karbar mulki.

Netanyahu dai bayyana kawancen a matsayin mai hadari ga zaman lafiyar Isra’ila.

 

3975389

 

Abubuwan Da Ya Shafa: netanyahu nasara kafa gwamnati Firaminista
captcha