IQNA

Cibiyar Fatawa Ta Azhar Ta Haramta Wasannin Kwamfuta Da Ake Rusa Kaba'abah Mai Tsarki

18:52 - June 30, 2021
Lambar Labari: 3486064
Tehran (IQNA) Cibiyar fatawa ta hanyar yanar gizo da ke karkashin cibiyar ilimi ta Azhar ta yi gargadi dangane da wasannin kwamfuta masu keta alfarmar dakin ka’abah.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, Cibiyar fatawa ta hanyar yanar gizo wati fatwa online, da ke karkashin cibiyar ilimi ta Azhar, ta yi gargadi dangane da wasu sabbin wasannin kwamfuta da aka kirkiro domin yara, wadanda suke a matsayin tozarci ne ga dakin ka’abah.

Bayanin ya ce, baya ga kasantuwar irin wadannan wasanni suna da mummunan tasiri da suke bari a cikin kwakwalen yara, saboda yadda ake yin kasashe da yake-yake, da sauran abubuwa na tashin hankali, a lokaci guda kuma za su zama masu tasiri mafi muni, idan wasannain suka danganci nuna kai hare-hare da rusa wurare masu tsarki na addini da hakan ya hada da dakin ka’abah.

Dakin Ka’abah wuri ne mai tsarki ga dukkanin musulmi, hatta wasu wadanda ba musulmi ba, suna girmama duk wani lamari da ya shafi Ka’abah, kasantuwar wannan daki a matsayi wuri na farko da aka fara ginawa a baya kasa, sannan kuma annabi Ibrahim da annabi Isma’il (AS) sun sake gina Ka’abah daga bisani, wanda hakan ke nuni da cewa wuri ne da yake da yake da tsarki a wurin dukkanin addinai na Allah.

 

3981091

 

 

captcha