
Shafin yada labarai Ahbar Yaum ya bayar da rahoton cewa, an nuna kwafin kur'ani tarjamar harsunan Swahili da Indonesia a bajen kolin littafai na birnin Alkahira na kasar Masar, wanda ake fansarwa da ragin kashi 50% na kudadensu.
Ministan harkokin addini na kasar Masar Muhammad Mukhtar Juma'a ya bayyana cewa, wannan babban baje koli yana da muhimmanci, kasantuwar ana samun littafai da aka tarjama a cikin harsuna daban-daban, daga ciki har kur'ani mai tsarki.
Ya kara da cewa ana nuna wasu daga cikin litatfai wadanda aka rubuta su da nufin daidaita tunanin matasa wadanda ake yaudarasu da sunan addini suna fadawa ayyukan ta'addanci.