
Jaridar Akhbar yau ta bayar da rahoton cewa, Samira Rajab wata tsohuwa ce 'yar shekaru 80 da haihuwa a kasar Masar, wadda har yanzu tana neman ilimi wadda kuma mahardaciyar kur'ani ce.
Wannan tsohuwa mai shelaru 80 a duniya ta bayyana cewa, ta kasance ba ta ita karatu da rubutu ba, saboda hakan ba za ta iya karanta rubutun kur'ani ba, amma jikokinta ne suka ba ta shawarar shiga makaranta yaki da jahilci, inda a nan ne ta koyi rubutu da karatu cikin kankanin lokaci.
Ta ce daga bayan lokacin tana iya karanta kur'ani ba tare da matsala ba, kuma duk da tsufa ya kama ta, amma ta kudiri aniyar fara yin hardar kur'ani mai tsarki, kuma bayan 'yan shekaru ta kammala hardar kur'ani baki daya a cikin watan ramadan da ya gabata.