
Shafin yada labarai an mawazin News ya bayar da rahoton cewa, hukumomi a lardin Najf sun sanar da cewa, tuni aka fara daukar dukkanin matakan da suka dace domin tarukan Ashura.
Bayanin ya ce daga cikin muhimman matakan da aka fara dauka ya zuwa yanzu dai akwai batun tsaro, musamman ganin yadda 'yan ta'adda masu kiyayya da iyalan gidan manzon Allah suka fara dawowa da hare-harensu a kasar.
Sannan kuma akwai matakai na kiwon lafiya, sakamakon yaduwar cutar corona, da kuma yadda za a dakile yaduwarta a tsakanin mahalarta tarukan.
A birnin Karbala kuwa tuni aka riga aka fara dukkanin shirye-shirye, musamman ma ganin cewa tarukan Ashura an fi gudanar da su a birnin, saboda tuni shirye-shirye sun yi nisa.
Daga cikin irin matakan da aka dauka har da saka kamarori kimanin dubu daya da dari shida a dukkanin sassan birnin domin sanya ido da kuma kula batun tsaro, da kuma samar da wurare na kula da lafiyar jama'a.