IQNA

Karatun Kur'ani Mai Tsarki Tare Da Marigayi Sheikh Shuhat Muhammad Anwar

Tehran (IQNA) karatun kur'ani mai tsarki tare da marigayi Sheikh Shuhat Muhammad Anwar inda yake karatun surat Furqan.

A cikin wannan faifan bidiyo marigayi Sheikh Shuhat Muhammad Anwar yana karatun ayoyi na 30 zuwa 33 a cikin surat Furqan.

An haifi sheikh Suhat ne a cikin shekara ta 1950 a lardin Dehqaliyya na kasar Masar, sannan ya hardace kur'ani mai tsarki yana da shekaru 8 da haihuwa.

Ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya da dama domin karatun kur'ani, da suka hada da Amurka, Burtaniya, Argentina, Spain, Brazil da dai sauransu.

Ya rasu ranar 13 ga watan janairu shekara ta 2008 bayan fama da wata rashin lafiya.