IQNA

Ra'isi: Gazawar Amurka A Afghanistan Dama Ce Ta Dawo Da Zaman Lafiya A Kasar

21:52 - August 17, 2021
Lambar Labari: 3486213
Ra'isi: Gazawar Amurka A Afghanistan Dama Ce Ta Dawo Da Zaman Lafiya A Kasar
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Iran bayyana cewa gazawar Amurka a Afghanistan wata dama ce ta wanzar da zaman lafiya a Afghanistan.

Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra'isi ya bayyana cewa gazawar Amurka a kasar Afghanistan, wata dama ce ta wanzar da zaman lafiya a Afghanistan.

A martanin farko da ya mayar bayan da ‘yan Taliban suka kwace iko da Kabul, shugaba Ra’isi, ya ce ya kamata ficewar sojojin Amurka, ya zama wata dama ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Aghanistan.

Ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin Afghanistan dasu cimma matsaya ta siyasa domin jagorancin kasar.

Iran, ta kuma ce a shirye ta ke ta taimaka wajen dawo da zaman lafiya a makobciyar kasar Afghanistan.

Dama dai Iran ta jima da take kalubalantar kasancewar sojojin Amurka a kasar ta Afghanistan dama yankin baki daya.

Iran dai na kallon kasancewar Amurka a yankin a matsayin barazana ga zaman lafiya da tsaro.

3991146

 

 

captcha