
Rahotanni daga kasar Iraki sun tabatar da da cewa, a yau an yi gumurzu tsakanin dakarun sa kai na Hashd Alshaabi da kuma wasu gungun 'yan ta'adda a yankin Tarimiyya da ke cikin gundumar Kazimiyya a kusa da birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.
Bangaren yada labarai na dakarun Nujba ya sanar da cewa, dakarun Nujba reshen rundnar sa kai ta Hashd Alshaabi ne suka yi gumurzun da 'yan ta'addan, kuma 4 daga cikin dakarun sa kan sun yi shahada.
Kungiyar Nujba na daya daga cikin muhimman bangarori na dakarun sa kai na Hashd Alshaabi a kasar Iraki, wadanda suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen fatattakar 'yan ta'addan Daesh a a kasar.
Sai a daya bangaren kuma an halaka adadi mai yawa na 'yan ta'addan an kuma kame wasu, wadanda za su bayyana a gaban kuliya domin fuskantar hukunci.
A cikin 'yan lokutan baya-bayan nan dai 'yan ta'addan Daesh sun fara dawowa da ayyukansu a wasu yankunan kasar Iraki, musamman ma tun bayan da al'ummar kasar Iraki suka fara matsa lamba a kan dole ne Amurka ta fice daga kasarsu.
Bangarorin tsaro na kasar Iraki sun sha bayar da bayanai kan yadda Amurka take gudanar da ayyuka na hadin gwiwa tare da 'yan ta'addan daesh a cikin kasar Iraki.