IQNA

Wani Dan Ta'adda Ya Daba Wa Mutane 6 Wuka A Kasar New Zealand

18:18 - September 03, 2021
Lambar Labari: 3486266
Tehran (IQNA) wani dan ta'adda ya daba wa mutane akalla 6 wuka a wani wurin sayayyar kayayyaki a kasar New Zealand.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, jami'an 'yan sandan kasar New Zealand sun sanar da cewa, a yau wani dan ta'adda ya daba wa mutane akalla 6 wuka a wani wurin sayayyar kayayyaki a kasar New Zealand.

Firayi ministar kasar New Zealand ta bayyana cewa, mutumin dan kasar Sri Lanka ne, kuma ya kwashe tsawon shekaru 10 yana zaune a kasar ta New Zealand, sannan kuma tun shekaru 5 da suka gabata ne jami'an tsaro suke sanya ido a kansa saboda take-takensa.

Ta ce mutumin ya tasirantu da ra'ayoyi na tsatsauran ra'ayi irin an 'yan ta'addan Daesh, wanda hakan yasa ake kallonsa a matsayin wanda zai iya aikata ta'addanci a kowane lokaci, kuam hakan ta faru.

Firayi ministar ta ce daga lokacin da ya kai harin  an kashe kasa da minti daya, duk kuwa da cewa dai ya raunata mutane ta hanyar daba musu wuka.

Jami'an tsaro sun ce ya shiga babban shagon New Lynn ne, inda ya fara daba wa mutane wuka, ya kuma jikkata mutane 6, kuma 3 daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.

 

3994762

 

captcha