Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jinjina wa 'yan wasan kasar kan nuna kwazon da suka yi a gasar motsa jiki ta nakasassu ta duniya.
Ga matanin sakon:
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Ina godiya matuka da kuma yin jinjina ga 'yan wasan Iran da suka nuna kwazo a a gasar motsa jiki ta nakasassu ta duniya wadanda suka faranta ran 'yan kasarsu ta hanyar samun lambobin yabo na zinariya.
Sayyid Ali Khamenei
4 Satumba 2021