IQNA

Taliban Ta Sanar da Cewa Ta Kammala Kwace Iko Da Panjshir 'Yan Gwagwarmaya Kuma Sun Karyata

20:49 - September 06, 2021
Lambar Labari: 3486278
Tehran (IQNA) kungiyar Taliban ta ce ta kammala kwace iko da jihar Panjshir a kasar Afhanistan

Majiyoyin kungiyar Taliban sun kungiyar ta kammala kwace iko da jihar Panjshir a kasar Afhanistan, bayan dauki ba dadi da mayakan kungiyar suka yi da magoya bayan Ahmad Mas'ud, wanda yaki mika kai ga kungiyar.

A cikin wani bayani da kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya yi ga mayakan kungiyar a cikin filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Kabul, ya bayyana cewa, an kawo karshen yaki a kasar, kuma sun shimfida ikonsu a jihar Panjshir wadda taki mika wuya.

Baya ga haka kuma kungiyar ta nuna hotunan bidiyo na babban ginin gwamnatin jihar Panjshir, inda mayakan kungiyar suka saukar da tutar kasar Afghanistan da ke wurin, suka dora tutarsu.

Sai dai a nasa bangaren Ahmad Mas'ud wanda ke jagorantar mayakan yankin na Panjshir wajen yin turjiya a gaban mayakan Taliban tare da kin mika wuya gare su ya karyata cewa Taliban ta kammala kwace iko da jihar baki daya.

Haka nan kuma ya yi ikirarin cewa, sunan nan cikin jihar kuma za su gaba da yaki da Taliban, kamar yadda ya bukaci al'ummar Afghanistan da su mike su kwaci 'yancin kansu daga mulkin mallakar Taliban.

 

3995468

 

 

 

captcha