IQNA

Matsalar Corona Ta Sa An Sake Rufe Masallatai Da Majami'oi A Togo

20:16 - September 10, 2021
Lambar Labari: 3486292
Tehran (IQNA) matsalar corona ta sanya a sake rufe masallatai da majami'oi a kasar Togo.

Shafin jaridar Punch ng ya bayar da rahoton cewa, sakamakon matsalar corona hakan ya sa a sake rufe masallatai da majami'oi a kasar Togo baki daya.

Rahoton ya ce, an dauki matakin ne bayan sake dawowar cutar a cikin kasar da kuma wasu kasashe makwabta da kasar Togo.

Wannan doka ta shafi dukkanin wuraren ibada, da hakan ya hada da masallatai da majami'oi gami da tarukan aure, da na janaza da kuma sauran taruka da suka shafi wasanni ko al'adu da sauransu ko siyasa.

A kasar Togo da ke yammacin Afirka mutane dubu 23 ne suka kamu da cutar corona yayin da mutane 203 kuma cutar ta yi ajalinsu.

 

 

3996462

 

 

 

 

 

captcha