IQNA

Kwamitin Gyaran Bugun Rubutun Kur'ani A Kasar Masar

19:08 - September 21, 2021
Lambar Labari: 3486334
Teharan (IQNA) kwamitin gyaran bugun rubutun kur'ani a kasar Masar na daga cikin dadaddun kwamitoci da suke karkashin cibiyar Azhar.

Shafin yada labarai an Sadal balad ya bayar da rahoton cewa, wamitin gyaran bugun rubutun kur'ani a kasar Masar na daga cikin dadaddun kwamitoci da suke karkashin cibiyar Azhar babbar cibiyar addinin muslunci ta kasar.

Babban aikin wannan kwamiti shi ne bin dukkanin matanonin kur'ani da ake bugawa kafin a fitar kwafinsu zuwa kasuwa, domin tabbatar da cewa abbu kurakurai a cikin bugun, a bangaren tsarin surori, da ayoyi da kuma kalmomi, har ma da wasulla.

Abdulkarim Ibrahim Saleh shugaban kwamitin ya bayyana cewa, akwai kalmomi wadanda bisa ga tsarin rubutun larabci ba su canjwa, amma wajen rubutun kur'ani akwai tsari na musamman da ake rubuta su, wanda kuma kur'ani ne kawai ya kebantu da haka sabanin dukkanin littafai na larabci.

Saleh ya ce wannan kwamiti ya kunshi manyan malamai daga cibiyar Azhar, da kuma masana kan ilmin harshen larabci da lugga da rubutu.

 

 

 

3999026

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha