IQNA

Baje Kolin Kur'ani A Kan Hanyar Masu Tattakin Arba'in A Iraki

21:11 - September 23, 2021
Lambar Labari: 3486344
Tehran (IQNA) ana gudanar da baje kolin kur'ani a kan hanyar masu tattakin arba'in na Imam Hussain (AS) a Iraki

Shafin yada labarai na Kafil ya bayar da rahoton cewa, ana gudanar da baje kolin kur'ani a kan hanyar masu tattakin arba'in na Imam Hussain (AS) zuwa Karbala a Iraki.

Wannan baje koli dai ya hada abubuwa daban-daban da suka shafi kur'ani mai tsarki, daga ciki har da nuna fasahar rubutun ayoyin kur'ani da salon rubutu mai kayatarwa a kan alluna.

baya ga haka kuma akwai bayanin tafsiran manyan malamai daban-daban, inda aka bijiro da wasu bangarori na tafsiran wasu ayoyi daga cikin littafan nasu nasu a wannan wuri.

Wannan dai shi ne karon farko da aka fara gudanar da irin wannan baje kolin ayyuka da suka shafi kur'ani da wannan salo a yayin tattakin ziyarar arba'in a Iraki.

 
Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha