
Shafin yada labarai na Almaaluma ya bayar da rahoton cewa, dakarun Hashd Alshaabi a kasar Iraki sun samu nasarar halaka wani babban kwamanda na 'yan ta'addan Daesh.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, dakarun Hashd al-Shaabi sun ce: Dakarun Tigris na Al-Hashd al-Shabi da ke da alaka da Operation Salahuddin, tare da hadin gwiwar bayanan ‘yan sandan tarayyar Iraki, sun sami nasarar cafke babban kwamnada na ‘yan ta’adda Idris Adnan Ismail wanda ake kira Abu Rahma.
Wannan kasurgumin dan ta’adda dais hi ne ke da alhakin tattara abin da ake kira zakka ga ISIL, an kuma samu nasarar damke shi ne a cikin a yankin Al-Nissan da ke kudancin Tikrit a gundumar Salahuddin.
Dakarum Al-Hashd al-Shabi sun jaddada cewa umurnin wannan aikin zai ci gaba da gudana da irin wannan salon a yin kwanton bauna da ayyukan hana kutsawar kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin birane, domin kauce wa barazanar tsaro ga 'yan kasar Iraki.
An dai kafa dakarun sa kai na Hashd Al shaabi ne biyo bayan fatawar da babban malamin addinin muslunci na Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya bayar kan hakan, domin murkushe ‘yan ta’addan daesh a lokacin da suka shigo kasara shekara ta 2014, inda matasa sama da miliyan 4 suka yi rijistar sunayensu domin shiga cikin rundunar, amma dai an dauki dubban daruruwa daga cikinsu bayan tantancewa.